Majalisar dokokin Birtaniya ta katse hutunta

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Firaministan Birtaniya David Cameron

Majalisar dokoki kan katse hutunta a lokutan da aka fuskanci rikici, wanan shine karo na ashirin da biyar da za'a yi haka a shekaru hamsin da suka wuce.

Sai dai ga fiministan kasar wanan shine karo na biyu a takaitaccen lokacin da ya rike da mulki da yan majalisar dokoki zasu katse hutunsu, na farko dai shine a lokacin da aka fuskanci badakalar saurare da karanta sakonin wayoyin salular jama'a.

Sai dai a bayane take cewa wanan wani batu me tada hankali sosai.

Sai dai babu wata gwamnati da zata so ta fuskanci batu me tada hankali kamar tabbatar da doka da oda da kuma lafiyar alumarta. Akan haka kalubalen dake gaban David Cameron shine tabartarwa 'yan majalisar da 'yan kasar gabakidaya akan cewa an fara shawo kan lamari.

Amma kalaman da suka fito daga bakinsa na nuni da cewa yan jam'iyyar masu ra'ayin rikau sun dora laifi akan barkewar tarzomar akan rashin sanin ya kamata da kuma son kai a maimakon halin kunci da jama'ar kasar ke ciki.

Bugu kari kuriar jin ra'yoyin jama'a na nuni da cewa wanan shine ra'ayin akasarin jama'ar kasar amma ta nuna cewar jama'a da dama sun yi amana gwamnati da 'yansanda sun yi sanyi jiki wurin shawo kan tarzomar ya zuwa yanzu.