Ra'ayi; Ko ya damunar bana ta zo muku?

Wasu manoma a jihar Kano, Nijeriya
Image caption Wasu manoma a jihar Kano, Nijeriya

Hakika wannan shekara ta zo wa nahiyar Afrika da kalubale iri-iri, amma wanda ya fi jan hankali a halin yanzu shi ne batun karancin abinci a yankin kusurwar Afrika, inda yanzu haka ake fama da matsanancin fari.

To a yammacin Afrika ma ga dukkan alamu akwai kalubale na rashin tsayawar damuna, inda a wasu sassa na yankin ake fama da kamfar ruwan sama .

Irin wadannan yankuna sun hada da wasu sassa na Jumhuriyar Nijar, da kuma wasu jihohin Arewacin Nijeriya.

Shin wane hali manoma suke ciki a halin yanzu; wanne irin tallafi kuma suke bukata domin ganin an samu kyawun amfanin gona?

Daga cikin wadanda muka gayyato domin tattaunawa kan wannan batu sun hada da: Dr Bukar Tijjani, minista a ma'aikatar ayyukan gona ta Najeriya,da Farfesa Muhammad Auwal Hussein, shugaban sashen kimiyyar aikin gona na jami'ar Bayero ta Kano, akwai kuma Malam Mamman Sani, Darakta a ma'aikatar ayyukan gona ta jamhuriyar Nijar, sai kuma masu saurare dake kan layi wadanda za su bayyana ra'ayoyinsu.