Hannayen jari a Turai sun dan farfado

Bayan mako guda da kasuwaanin hannayen jari suka yi suna tangal tangal a kasashen duniya, kasuwannin hannayen jari sun dan farfado a yau a Turai, abunda ya dan maida asarar da aka tafka ranar litinin.

Kasuwar hada hadar hannayen jarin New York ta Amurka ta yi ta tangal tangal yanzu ta samu sa'ida.

Wakilin BBC yace koda yake hakan zai kwantar wa masu saka jari hankali, matsalar da ake fuskanata a kasuwannin hannayen jari, manuniya ce ga irin damuwarda ake nunawa akan yanayin tattalin arziki a Turai da Amurka.

Kuma akwai fargabar cewa masu saka jari zasu yanke kauna da lamarin bankuna.