Hannayen jari sun tashi bayan haranta zamba cikin aminci

An fara aiki da wani haramci da aka sawa wani salon cinikin hannayen jarin bankuna da wasu cibiyoyin kudi a wasu kashen turai.

Kasahen faransa, da Italia, da Belguim da kuma Spain, sun haramta wannan salon cinikin na makonnin biyu bayan darajar hannayen jari a kasahen sunyi kasa

A salon cikin dai, masu sai da hannayen jari, kan ci riba ne bisa hasashen cewa darajar hannun jari zatayi kasa.

Minstan kudin Faransa Francois ya bayyana haramcin da cewar; "ai masu wannan salon ciniki kamar kububuwa suke da sun sareka sai su bace. Nayi maraba da harancin da aka sanar a daren jiya"

Sai dai kamar yadda Hausawa kan ce, Faduwar wani, tashin wani",a Najeriya, hannayen jari sun samu tagomashi a kasuwannin hada-hadar hannayen jarin kasar a karon farko tun farkon watan Agustan da muke ciki.

A jiya dai, hannayen jarin sun tashi da digo ashirin da hudu cikin dari, kuma a yau ma kasuwar na dada samun tagomashi, abin da masu hada-hada a kasuwar sai da hannayen jarin kasar suka ce ya faru ne saboda faduwar da kasuwannin hannayen jarin Turai ke ci gaba da yi.