An kashe fararen hula ashirin da hudu a Syria

Image caption Shugaba Bashar Al'asad na Syria

'Yan adawa a Syria sun ce, jami'an tsaro sun kashe a kalla fareren hula ashirin da hudu jiya alhamis, yayin da hukumomin kasar ke cigaba da kokarin murkushe zanga-zangar nuna adawa da gwamnati.

Jami'an tsaron sun aikata yawancin kisan ne a garin Qusair dake kusa da iyaka da Lebanon:

An kuma samu rahotannin karin zanga-zanga a yankuna da dama bayan sallar asuba, sai dai kuma jami'an tsaro sun yi ta budewa masu zanga-zangar wuta.

Sai dai Sakatariyar hulda da kasashen wajen Amurka, Hillary Clinton tayi kira ga sauran kasashe su bi sahun Amurka wajen azawa Syria takunkumi, saboda yadda jami'an tsaron kasar ke amfani da karfi akan al'ummar kasar.

Hillary Clinton ta kuma ce, musamman ma China da India zasu iya tallafawa wajen matsa lamba ga Shugaba Bashar Assad saboda irin jarin da suka zuba a fannin makamashi na kasar ta Syria