EFCC ta mika wani dan Najeriya ga Amurka

Tambarin Hukumar EFCC
Image caption Tambarin Hukumar EFCC ta Najeriya

A Najeriya, Hukumar Yaki da Yiwa Tattalin Arzikin Kasa Zagon Kasa, wato EFCC, ta tasa keyar wani dan kasar, Mista Emmanuel Ekhator, zuwa kasar Amurka domin ya amsa wasu laifuffuka da suka danganci zamba.

Mahukanta Amurka sun nemi Najeriya da ta tuso keyar mutumin ne bayan wata kotu a kasar ta same shi da laifin aikata zamba a kasar a shekara ta 2010.

Hukumar EFCC dai ta ce Mista Emmanuel ya damfari wasu cibiyoyin lauyoyi ne a Amurkan kudin da suka kai dalar Amurka miliyan talatin da daya.

Masu shigar da kara a kasar ta Amurka sun ce mutumin ya damfari cibiyoyi akalla tamanin ta hanayr ba su cakinkudi na bogi.

Har wayau an zarge shi da laifin hulda da wani gugun mazambata wadanda ke kokarin damfarar akalla mutane dari uku.