Matakan tsuke bakin aljihun gwamnatin Italiya

Image caption Majalisar ministocin Italiya

Majalisar ministocin Italiya ta amince da abin da firayim ministan kasar, Silvio Berlusconi, ya kira matakan tsuke bakin aljihun gwamnati masu tsaurin gaske wadanda za su taimaka wajen inganta asusun gwamnati, kuma su rage gibi a kasafin kudin kasar.

Bisa wannan tsari dai, badi gwamnatin ta Italiya za ta rage Euro biliyan ashirin daga kudaden da ta saba kashewa, kuma za a kara zaftare Euro biliyan ashirin da biyar a shekara ta 2013.

Sai dai duk da cewa gwamnatin kasar ba ta ce komai a kan batun kara haraji ga masu hannu da shuni ba, ta kara kudin haraji ga wadanda ke karbar albashi mai tsoka da kashi goma cikin dari yayinda da kudin ruwa ya karu da kashi bakwai da rabi a cikin dari.

Za a rasa guraben ayyunkan yi dubu hamsin a matakin kananan hukokomin kasar amma ba a bayyana lokacin da za a fara korar ma'aikanta ba.

Bugu da kari shugabannin kananan hukomomi sun nuna adawarsu da matakan tsuke bakin aljihun gwamnati na gaggawa wadanda suka ce fanin ilmi, kiwon lafiya da hanyoyi za su fuskanci komabaya sakamakon kudaden da za a zaftare.

Sai dai matakan za su fara aiki ne idan Majalisar Dokokin kasar ta amince da su nan da kwanaki sittin.