Somaliya za ta kirkiro runduna ta musamman

Firayim Ministan Somalia Abdiweli Mohamed Ali
Image caption Firayim Ministan Somalia Abdiweli Mohamed Ali

Firayim Ministan Somaliya ya bayar da sanarwar kirkiro wata runduna ta musamman wadda za ta rika bayar da kariya ga jerin gwanon motocin da ke kai kayan agaji ga wadanda fari da yunwa ke shafa.

Firayim Minista Abdiweli Mohamed Ali ya bayyana haka ne bayan ganawa da babbar jami'ar Majalisar Dinkin Duniya mai kula da raba kayan agajin gaggawa, Valerie Amos, a Mogadishu, babban birnin kasar ta Somaliya.

A cewarsa, a tashin farko rundunar za ta kunshi sojoji dari uku, wadanda za su horo na musamman kuma su samu taimako rundunar kiyaye zaman lafiya ta Tarayyar Afirka.

Mista Ali ya ce manayn ayyukan rundunar guda biyu ne:

"Na farko shi ne su tsare ayarin motocin, su kuma kare agajin abinci; sannan kuma su ba da kariya ga sansanoni yayin da ake rabon abincin.

"Na biyu kuma shi ne su tabbatar da zaman lafiya a birnin Mogadishu sannan su yaki 'yan daba da masu kwasar ganima da sauran kazanta".

Majalisar Dinkin Duniyar ta ce mutane kimanin miliyan sha biyu ne matsalar yunwa da ta fari a kusurwar gabashin Afrika ke shafa.