Gwamnan Texas zai nemi shugabancin Amurka

Rick Perry yana bayyana aniyarsa Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Gwamnan Jihar Texas, Rick Perry, yana bayyana aniyarsa ta tsayawa

Gwamnan Jihar Texas ta Amurka, Rick Perry, ya tabbatar da cewa zai tsaya neman takarar shugabancin kasar a karkashin jam'iyyar Republican a zaben shugaban kasa na badi.

Mista Perry ya gabatar da jawabin tsayawa takarar ta sa ne cikin shewa da tafi daga magoya bayansa.

Ana dai ganin Mista Perry a matsayin wani dan takara wanda za a fafata da shi domin zai iya hada kan masu matsakaici da kuma ra'ayin rikau na jam'iyyar ta Republican.

Sanarwar ta Mista Perry ta zo ne a daidai lokacin da mutane takwas din da ke son yiwa jam'iyyar ta Republican takara ke fuskantar wata kuri'ar jin ra'ayin jama'a a Jihar Iowa wadda za ta iya yin tasiri wajen fitar da dan takarar da a karshe zai kalubalanci Shugaba Obama.

Kuri'ar jin ra'ayin jama'ar Amurka dai ta nuna cewa tsohon gwamnan Jihar Massachusetts, Mitt Romney, ne kan gaba a cikin 'yan takarar.