Aung San Suu Kyi na gudanar da wata ziyara

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Aung San Suu Kyi

Jagorar tabbatar da dimokaradiyya a Burma, Aung San Suu Kyi, za ta yi tafiya zuwa wajen birnin Rangoon a karo na farko tun bayan dage daurin talalar da aka yi mata a watan Nuwamban da ya gabata.

Za dai ta je yankin Bago ne mai nisan kilomita hamsin a arewa da birnin, inda za ta gana da magoya bayanta.

Wani kakakin jam'iyyarta ta National League for Democracy ya ce Aung San Suu Kyi za ta kaddamar da wasu dakunan karatu guda biyu sannan kuma ta gana da mambobin wata majalisar matasa.

A ziyarar karshe da ta kai wani yanki na karkara a shekarar 2003, an yiwa ayarin motocin da ta ke ciki kwanton-bauna, al'amarin da ya kai ga tsare ta har tsawon shekaru bakwai.