An yi yunkurin tayar da bam a Maiduguri

Rahotanni daga Maiduguri babban birnin jihar Borno na cewa jami'an tsaro sun tabbatar da bindige wani mutum har lahira a hedkwatar 'yan sandan jihar.

Ana zarginsa ne da yunkurin tayar da bam a hedkwatar 'yan sandan yayinda ake daukar wasu sabbin 'yan sanda aiki.

Hakan na faruwa ne 'yan watanni bayan harin bam da aka kai a babbar hedkwatar 'yan sandan Nijeriyar dake Abuja, lamarin da ya haddasa asarar rayuka, da dukiyoyi.

Shi dai harin na baya, kungiyar jama'atu ahlul sunna lid da'awati wal jihad da aka fi sani da suna Boko Haram, ta amsa cewa ita ta kai shi.