Mubarak zai sake bayyana a kotu

Image caption Hosni Mubarak a yayin da ya bayyana a kotu

A yau Litinin ne ake sa ran tsohon shugaban Masar, Hosni Mubarak, zai sake bayyana a gaban kotu a ci gaba da tuhumarsa da ake yi da laifin almundahana da bayar da umarnin kashe masu zanga-zanga a boren da aka yi a kasar a farkon bana.

Mista Mubarak dai, wanda aka ba da rahoton cewa yana fama da rashin lafiya, ya bayyana ne a kan gadon daukar marasa lafiya lokacin da kotun ta bude zamanta a farkon wannan watan.

Sai dai tsohon shugaban na Masar ya ki amincewa da tuhume-tuhumen da ake yi masa.

Daruruwan mutane ne dai aka kashe a yayin da suke bore don matsantawa tsohon shugaban kasar sauka daga kan mulki a farkon shekarar da muke ciki.