Hosni Mubarak ya sake bayyana a kotu

Image caption Hosni Mubarak a yayin da ya bayyana a kotu

Tsohon shugaban kasar Masar Hosni Mubarak ya sake bayyana a gaban kotu a ci gaba da tuhumarsa da ake yi da laifin almundahana da umarnin kashe masu zanga-zanga.

Mr Mubarak, mai shekaru 83 na fuskantar hukuncin kisa idan aka same shi da laifin bada umarnin kisan masu zanga-zanga a farkon shekaran nan.

An sake kawo shi kotun ne a gadon daukar marasa lafiya, inda ya ke magana da 'ya'yansa Alaa da kuma Gamal.

Alaa da Gamal wadanda ke fuskantar shari'ar cin hanci da rashawa sun musanta tuhumar da ake yi musu.

Mr Mubarak ya bar gadon mulki ne bayan mummunar zanga-zangar adawa da shugabancinsa a watan Fabreru.

Editan BBC a gabas ta tsakiya Jeremmy Bowen ya ce, Mr Mubarak yana da tasiri sosai a kasar, kuma shari'ar ce za ta nuna irin sabuwar alkiblar da kasar ta Masar za ta fuskanta nan gaba.

Dubban masu adawa da shi da kuma magoya bayansa sun taru a wajen kotun, inda ake samun 'yar tarzoma.