Human Rights Watch ta soki rikicin Somalia

Image caption Taswirar kungiyar Human Rights Watch

Kungiyar kare hakkin bil- Adama ta Human Rights Watch ta zargi bangarorin da ke fada da juna a Somaliya da yiwa dokokin kasa-da-kasa karan tsaye.

A wani sabon rahoto da ta wallafa, kungiyar ta ce keta hakkokin bil-Adama na taimakawa wajen kazantar bala'in da ake fama da shi a kasar.

Ta yi kira ga bangarorin su kawo karshen cin zarafin jama'a su kuma tabbatar da cewa kayan agaji na kaiwa ga mabukata.

Mawallafa rahoton sun zargi kungiyar masu kishin Musulunci ta Al Shabab da musaganawa fararen hula da kuma gallaza musu ba kakkautawa a yankunan da ke karkashin ikonta.

Ita kuwa Gwamnatin Rikon Kwarya ta kasar an zarge ta ne da kama mutane da kuma tsare su ba gaira ba dalili.

Sai dai mai magana da yawun gwamnatin, Abdi Rashid Aseed, ya ce ba kanshin gaskiya a wannan batu:

''Wannan batu ba gaskiya ba ne saboda a Kenya aka tattaro wadannan bayanan. Mun gayyaci kungiyoyin kare hakkin bil-Adama masu mutunci irin su Afirka Watch su zo Mogadishu da sauran wuraren da gwamnati ke da iko; kuma ma kafin makon da ya gabata ai gwamnati ba ta iko da dukkan sassan birnin na Mogadishu''.