Rikicin kasar Syria na kazancewa

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Latakiya

Wani mazaunin Latakia da ke Syria ya bayar da shaidar yadda dakarun gwamnati suka yi ta barin wuta a kan masu fafutukar tabbatar da dimokaradiyya a garin.

Mutumin mai suna Fua'd ya shaidawa BBC cewa yana kallo daga rufin gidansa yayin da sojojin gwamnatin suka yi dirar-mikiya a kan wadansu unguwanni bayan sun yi luguden wuta da tankuna, da kuma kananan jiragen ruwan yaki, ta hanyar amfani da manyan bindigogi.

''Tun da misalin karfe shida na safiya sojoji suka fara barin wuta ta hanyar amfani da manya da kananan makamai.

''Mun ji karar fashewar abubuwa unguwannin Al-Raml da Masbah Al-Shab, inda sojojin ke yunkurin kutsawa ta hanyoyi uku''.

A cewar mutumin an tabbatar da mutuwar mutane akalla ashirin da takwas yayin da wadansu da dama suka jikkata.