Gwamnati za ta karbi karin bankuna a Nijeriya

Image caption Gwamnan babban bankin Nijeriya Sanusi Lamido

Rahotanni daga Nijeria sun ce hukumar gudanar da kadarorin gwamnatin kasar, AMCON ta ce tana sa ran ragowar bankuna biyar daga cikin bankuna 9 da aka ceto a shekara ta 2009, za su gudanar da manyan tarurukansu na musamman nan da ranar 30 ga watan Satumba, domin masu hannyen jari a bankuna su amince da batun karfafa jarin bankunan. An ruwaito shugaban Hukumar ta AMCON, Mustapha Chike-Obi yana cewa yana sa ran masu hannayen jari a bankunan za su amince da 'yarjejeniyar da bankunan suka kulla da masu saka jari. Ya ce idan baa haka ba, to Hukumar ta AMCON za ta duba duka hanyoyin da suka dace, don kare kudaden ajiyar jamaa da ma'aikatan bankunan da kuma tsarin tattalin arzikin kasar. Bankunan dai sun hada da Intercontinental Bank da Oceanik Bank da Finbank da Union bank da kuma Equitorial Trust bank. A cikin wannan watan ma, Hukumar ta AMCON ta karbe ikon gudanar da bankuna 3 daga cikin 9 din, bayan da suka gaza nuna alamun karfafa jarin nasu.