Cote d 'Ivoire ta sake bude gidan kaso a Abidjan

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Shugaba Alassane Ouattara na Cote d 'Ivoire

Kasar Ivory Coast ta sake bude babban gidan kason garin Abidjan bayan watanni biyar da rufe shi a saboda fasa gidan yarin da aka yi a lokacin. An mayar da 'Yan gidan kason farko su goma sha shida wani sansani na soji, domin yin gyara a gidan kason, wanda aka gina shi domin daukar fursunoni dubu daya da dariuku. Fiye da fursunoni dubu biyar ne dai suke tsere daga gidan kason a lokacin yakin basasar da aka yi a kasar ta Ivory Coast a watan Maris din daya gabata.