Shugabar IMF ta gargadi kasashen duniya

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Christine Lagarde

Shugabar Asusun ba da Lamuni na Duniya, IMF, Christine Lagarde, ta ce ya zama wajibi gwamnatoci su daidaita rage kashe kudade da kuma tallafi na matsakaicin zango ga bangarorin da ke kawo ci gaban tattalin arziki.

Ta ce hakan ne kawai zai sanya su kaucewa hatsarin sake fuskantar koma-bayan tattalin arziki.

A wata kasida da ta wallafa a jaridar Financial Times, Mis Lagarde ta amince cewa akwai bukatar maido da manufofin kashe kudade masu dorewa ta hanyar daidaita yawan basussukan da gwamnatoci ke karba.

Sai dai ta ce matse bakin aljihu cikin gaggawa ka iya tadiye farfadowar tattalin arzikin kasashe ya kuma tsananta rashin ayyukan yi.