Kalubalen tabbatar da tsaro a Najeriya

'Yin  adalci ne kawai zai tabbatar da  tsaro a Najeriya' Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Irin ta'adin da bam ya yi a Hedkwatar 'yan sandan Najeriya

A Najeriya, lamarin tsaro na ci gaba da tabarbarewa sakamakon hare-haren da 'yan bindiga ke kai wa a wadansu sassan kasar.

Ko a jiya Litinin, wadansu mutane wadanda ba a san ko su wanene ba sun kai hare-hare a jihohin Bauchi da Sokoto.

Kazalika wani mutum ya yi yunkurin tayar da bam a hedikwatar 'yansanda a jihar Borno, duk da yake hakan bai yi nasara ba.

A jiya ma hukumomi a kasar sun tabbatar da mutuwar mutane da dama sakamakon wata hatsaniya da ta auku a jihar Filato.

Akasarin tashe-tashen hankulan dai suna da dangantaka da kabilanci, da addini, da kuma siyasa.

Sai dai wani mai sharhi a fannin tsaro, Dokta Bawa Wase, ya shaidawa BBC cewa hare-haren na faruwa ne sakamakon rashin aikin yi, da kuma mawuyacin halin tattalin arzikin da akasarin 'yan kasar ke ciki.

Ya yi kira ga gwamnati ta samar da hanyoyin magance irin wadannan rikice-rikice domin samun dawwamammen zaman lafiya.