Amurka ta ce Shugaban Syria ya sauka

Shugaba Assad

Kasashen Amruka da Birtaniya da Faransa da Jamus sun yi kira ga shugaba Basshar Al-Asad na Syria da ya sauka daga mulki, bayan irin zanag-zangar da aka yi ta nuna adawa da mulkinsa a kasar ta Syria.

Wannan shi ne kira na farko baro-baro daga Amruka da kawayenta kan Mr Assad ya sauka daga mulki.

Ko da yake dai a baya Amruka ta ce abubuwa zasu fi tafiya a Syria ba tare da Mr Assad ba.

Shugaba Obama yace Mr Assad yayi kuskure idan yayi tunanin cewa zai iya toshe bakin jama'ar kasarsa.

Shugaba Obama kuma ya dakatar da yin amfani da kadarorin kasar Syria ga gwamnatin shugaba Asad, da kuma daina shigo da man fetur da Syria zuwa Amruka. Ga rahoton da Isa Sanusi ya hada mana.