Ana bikin kaddamar da tauraron dan Adam

Image caption Taswirar Najeriya

A yau Laraba ne Najeriya ke kaddamar da wani tauraron dan Adam mai suna Nigeria Sat-2.

Za a kaddamar da tauraron dan Adam din ne a kasar Rasha tare da wani tauraron mai suna Nigeria Sat-X wadanda za su rika aiko da bayanai daga sararin samaniya.

Hukumar Binciken Sararin Samaniya ta kasar ta ce daya daga cikin wadannan taurarin shi ne na farko da Injiniyoyi 'yan asalin kasar suka yi da kansu.

Shugaban Hukumar, Sa'idu Mohammed, ya shaidawa wa BBC cewa za a yi amfani da taurarin dan Adam din ne wajen bunkasa aikin gona, da samar da tsaro, da dai makamantansu.