An yi zanga zangar nuna kyamar cin hanci a Indiya

Dubban jamaa sun zanag-zanga a tsakiyar Delhi, babban birnin India, domin nuna goyon baya ga dattijon nan mai fafitikar yaki da cin hanci da rashawa, Anna Hazare.

Masu zanga-zangar, sun yi maci daga India Gate zuwa Ginin Mjalisar dokokin kasar.

Sauran magoya bayan Mr Hazare kuma sun taru ne a wajen gidan kurkukun da ake tsare da shi tun jiya Talata. Hakazalika an gudanar da jerin zanga-zanga irin wannan a birane daban-daban na Indiar.

Abhinandran Sekhri, shi ne kakakin kungiyar Mr Hazare ta India Agaist Corruption,ya ce,"gwamnati ta nuna cewa ba da gaske take ba a kan wannan shirin doka na yaki da cin hanci. Abun da take nema ta yi kawai shi ne kawar da kungiyarmu; amma abun da ba ta sani ba, shi ne yanzu kungiyar mu ta yi karfi, saboda haka ba za ta yi nasara ba."

Sai dai Pira minista, Manmohan Singh ya yi kakkausar suuka ga Mr Hazare, yana mai zargin shi da yunkurin kawo cikas ga Demokradiyya.