An kafa Majalisar kula da tattalin arzikin Najeriya

Goodluck Jonathan Hakkin mallakar hoto AP
Image caption A watan Mayun da ya gabata ne aka rantsar da Mr Jonathan

Shugaban Najeriya Dr Goodluck Jonathan ya kafa majalisar kula da tattalin arzikin kasar mai mambobi 24 - inda za ta kasance karkashin jagorancinsa.

Sanarwar da ta fito daga ofishin shugaban ta ce Mataimakin shugaban kasa Muhammad Namadi Sambo ne zai kasance mataimaki.

Yayin da ministar kudi da kuma tattalin arziki Ngozi Okonjo-Iweala za ta lura da gudanar da ayyukan majalisar.

Har ila yau kuma akwai Ministan tsare-tsare Dr Shamsudden Usman, da na kasuwanci da zuba jari Dr Olusegun Aganga da shugaban babban bankin kasar Sanusi Lamido Sanusi.

Wasu daga cikin mambobin:

Ministan samar da wutar lantarki Ministar ilimi Ministar man fetur Ministan ayyukan gona Ministan Lafiya Karamin ministan kudi Shugaban ofishin kula basuka na kasa Shugaban ofishin kula da kasafin kudi Mai baiwa shugaban kasa shawara kan tattalin arziki Da kuma gwamnonin jihohin Adamawa da Anambra

A ranar Alhamis za a kaddamar da Majalisar.

Karin bayani