Kungiyar OIC ta yi alkawarin kudi ga Somalia

Tambarin kungiyar kasashen musulmi ta OIC Hakkin mallakar hoto 5
Image caption Tambarin kungiyar kasashen musulmi ta OIC

Kungiyar kasashen Musulmai ta OIC ta yi alkawarin bada gudunmayar dala miliyan dari 3 da 50 ga yunkurin da ake yi na taimakawa masu fama da yunwa a Somalia.

A lokacin taron da kungiyar ta yi a birnin Satambul na Turkiya, mahalarta taron sun saurari Pira ministan kasar ta Turkiya, Rejep Tayyip Erdohan, yana suukar kasashe masu hannu da shuni,ya ce,"ya kamata a dauki batun taimakawa al'ummar Somalia, kamar wani gwaji na sanin ya kamata daga BilAdama. Duka kasashe yau suna fuskantar wani kalubale, kuma duka wannan, rashin adalci ne ke janyo shi."

A Turkiyyar kanta, gwamnati ta ce jamaar kasar sun bada tallafi da yawan shi ya dala miliyan dari da 15.

An shirya Mr Erdohan zai ziyarci kasar ta Somalia nan gaba a cikin wannan makon, don jagorantar aikin bada agajin da Turkiya ke yi.