'Yantawayen Libya sun kwace matatar Zawiyah

'Yan tawayen Libya sun karbe iko da wata matatar man petur dake wajen garin Zawiya.

Wasu manema labaru a inda lamarin ya auku , sun ce 'yan tawayen sun fatattaki dakarun Kanar Gaddafi daga yankin bayan sa'o'i biyar da aka kwashe ana artabu.

Wakilin BBC ya ce, kwace wannan matatar man petur, ba karamin koma-baya ba ne ga magoya bayan Kanar Gaddafi, ta fuskar tsare tsare da kuma kwarin gwiwarsu.

Idan dai 'yan tawayen zasu iya kare matatar man, hakan zai kasance, babban karsashi gare su, bayan da suka dade suna kawazucin kame ta.