'Yan sanda sun yi artabu da masu zanga zanga a Spain

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Masu zanga zanga a Spain

Yan sanda a kasar Spain sun yi taho mu gama da masu zanga zanga a Madrid babban birnin kasar, bayanda dubban mutane suka hau kan tituna su na jerin gwano sakamakon ziyarar da Paparoma ke shirin kaiwa kasar.

Masu zanga zangar wadanda suka fusata, saboda irin kudin da za a kashe akan ziyarar, sun hau kan tituna ne, suka doshi dandalin dake cibiyar birnin wato Sol square, inda suka hadu da masu ziyarar bauta da dama.

Yan sanda sun yi kokarin share dandalin inda a nan take aka fara dauki ba dadi saidai sun kama wasu daga cikin masu zanga zangar.

Idan an jima a yau ne Paparoma Benedict zai halarci wani taron matasa masu bauta daga sassan duniyanan daban daban.

Ziyarar tasa na zuwa ne a dai dai lokacin da gwamnatin ke shirin zaftare kudaden take kashewa duk dacewa wadanda suka shirya taron sun ce babu sisin gwamnati wurin shirya taron.