Mutane takwas suka halaka a Afghanistan

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Wurin da aka kaiwa hari

Maharan kunar bakin wake sun aukawa ofishin raya aladu na Birtaniya wato British Council dake Kabul babban birnin kasar Afghanistan, inda suka halaka mutane a kalla 8, wadanda yawancinsu yan sanda ne.

Mutane kimanin shidda ne dauke da manyan bindigogi masu sarrafa kansu da rokoki da gurneti suka aukawa ginin da ofishin British Council din yake.

Kuma anyi ta jin karar aman wuta a ginin.

Wakilin BBC yace tuni dakarun Birtaniya suka isa wurin.

Yau Juma'a ce dai ranar bukin zagayowar samun yancin kai na Afghanistan daga turawan mulkin mallaka na Birtaniya.

Taliban ta ce ta kai harin ne don wannan rana.