An dakatar da Ayo Salami daga aiki

A wata sanarwa da hukumar dake sa ido akan al'amura sharia ta Nigeria ta fitar a jiya ga manema labaru ta ce ta dakatar da shugaban kotun daukaka kara ta Nigeria Justice Ayo Salami daga aiki.

Hukumar ta kuma umurci Mr Salami akan ya mika aiyukan kotun zuwa ga wani babban alkali .

Bugu da kari hukumar ta bada shawara ga shugaban kasan Najeriya akan ya yi masa retiya daga aiki.

Duk da cewa hukumar bata ce komai ba akan dalilin da ya sa ta dakatar da Shugaban kotun daukaka karar amma masana kan al'amurar sharia a kasar na ganin hakan ba zai rasa nasaba da tankiyar dake tsakanin Mr Ayo Salami da kuma babban joji kasar Aloysius Katsina Alu.

Shi dai Salami na zargin babban jojin kasar da yunkurin sa baki akan shariar zaben gwamnan jihar Sokoto abun da kuma ya musanta

Hukumar ta debarwa Mr Salami wa'adin makon guda akan ya nemi afuwa daga wurin babban jojin kasar amma kuma be yi haka ba.

Sai dai wanan mataki da hukumar ta dauka na zuwa ne a dai dai lokacin da wata babbar kotu a kasar ke saurar karar da Mr salami ya shigar a gabanta.