Fira ministan Turkiyya na ziyara a Somalia

Tayyib Erdogan
Image caption Erdogan ne shugaban siyasa na farko da ya je kasar cikin shekaru 20

Fira ministan Turkiyya, Recep Tayyib Erdogan ya isa Mogadishu, babban birnin Somalia, a wani yunkuri na janyo hankalin kasashen duniya game da mummunar matsalar yunwar da ake fama da ita a yankin.

Mr Erdogan ne wani shugaban siyasa na farko daga wajen nahiyar Afrika, da ya kai zira kasar ta Somalia a cikin shekaru 20 din da suka wuce.

Ziyarar ta shi ta biyo bayan alkawalin da kungiyar kasashen Larabawa, OIC ta yi a farkon wannan makon, na bada agajin dala miliyan dari 350, don taimakawa wadanda ke fama da yunwa a yankin Kusurwar Gabashin Afrika.

Sai dai ziyarar ta Tayyip Erdogan ta so ta fara da kafar hagu, bayan da fiffikin daya daga cikin jiragen da ke dauke da wasu daga cikin 'yan tawagarsa, ta karci kasa lokacin da yake sauka a filin saukar jiragen sama na Mogadishu.

Goyon baya ga gwamnatin riko

Amma ziyarar ta ci gaba kamar yadda aka tsara. Turkiyya na maida hankali kan batun Somalia, a wani yunkuri na tallafawa jama'ar da ke fama da matsalar yunwar da ta dabai-baye Gabashin Afrika.

Mr Erdogan zai ziyarci wasu sansanoni da kungiyar Red Crescent ta Turkiyya ta kafa a Mogadishu, inda zai ganewa idanunsa rabon kayan abinci ga mutanen da yunwa ta raba da gidajensu.

Rahotanni sun kuma bayyana cewa Fira Ministan ya yi alkawarin cewa Turkyya za ta kafa wasu cibiyoyin wucin gadi a yankin.

Har ila yau ziyarar wata alama ce ta irin goyon bayan da Turkiyya ke nuna wa ga gwamnatin rikon kasar Somalia wacce ke tangal-tangal.

Sai a 'yan kwanakinnan ne gwamnatin rikon ta iya samun damar sake karbe iko da birnin Mogadishu bayan da mayakan al-Shabab suka fice makonni biyu da suka gabata.