Gaddafi ya yi jawabi ta rediwo

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Rahotanni sun ce, Kanar Gaddafi yayi jawabi ta rediyo, ga mazauna birnin Sirte - inda nan ne mahaifarsa - yana kira ga jama'a da kada su mika wuya ga dakarun tawaye.

Mazauna Sirte din sun gayawa 'yan uwansu da ke birnin Benghazi cewa, wani gidan rediyo na yankin ya watsa jawabin, wanda a cikinsa Kanar Gaddafin ke gargadin 'yan Sirte din da cewa, wa'adin da 'yan tawaye suka basu, na su yi saranda kan nan kan ranar Asabar, shigo-shigo ba zurfi ce.

Majiyoyi a Sirte sun ce, babu gas ko wutar lantarki a birnin, kuma kayayakin abinci suna karewa: