Gaddafi na Tripoli inji 'yan tawaye

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Shugabannin 'yan tawaye a Libya sun ce sunyi imanin cewa Kanar Gaddafi na boye kusa da babban birnin kasar

'Yan tawayen sun ce bayanan da suka samu sun samo asali ne daga shige da fice jama'a, hirarraki da suka kaste ta waya da kuma sauran bayanan sirri.

Wani jigo a bangaren 'yan tawayen ya ce da gaddafi baya Tripoli, to da ya tsere zuwa iyakar kasar da algeria saboda duk a kasashen da ke makwabtaka ta da Libya, algeria ce kasar da zata iya bashi mafaka.