An kai hari a Gombi, a arewacin Nigeria

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Rahotanni daga Nigeria na cewa wasu mutane dauke da makamai sun kai hari a wani ofishin 'yan sanda da kuma wasu bankuna da ranar yau a garin Gombi dake cikin Jihar Adamawa ta arewacin kasar.

Kawo yanzu dai ba a tantance ko su waye ne mutanen ba, sai dai wadanda suka shaidi lamarin sun ce sun kai harin ne yayinda suke ta kabbara.

Wasu rahotannin da ba a tabbatar da su ba sun ce mutanen da suka mutu sun kai 16.