Iran ta daure wasu Amurkawa

Gidan talabijin na Iran ya ce an yanke hukuncin daurin shekaru takwas a kan wasu Amurkawa matasa su biyu, bisa zargin shiga kasar ba bisa ka'ida ba, da kuma leken asiri.

Shekaru biyu da suka wuce ne aka kama mutanen biyu, Shane Bauer da Josh Fattal, da wata abokiyar tafiyarsu da aka bada beli, bayan da suka tsallaka kan iyaka suka shiga kasar da Iraki