Isra'ila ta dena kai hari- larabawa

Hakkin mallakar hoto Reuters

Wani taron gaggawa na kungiyar kasashen Larabawa ya yi Allah wadai da farmakin da Isra'ila ke kaiwa ta sama a Zirin Gaza.

Taron yace yakamata Majalisar Dinkin Duniya ta dauki wani mataki domin kawo karshen hare haren.

Hare haren Isra'ilar, wadanda suka haddasa mutuwar mutane akalla goma sha biyar, ya biyo bayan farmakin da wasu Palasdinawa 'yan bindiga suka kai ne, suka kashe 'yan Isra'ila takwas, ranar Alhamis.