Dokar hana yawon dare a Kafanchan

A Najeriya an kafa dokar hana yawon dare a garin Kafanchan na jahar Kaduna, bayan wani tashin hankali, a lokacin bukukuwan Sallah.

Rahotanni sun ce, wasu mutane ne da ba a tantance ba, suka kai hari ga jerin gwanon dawakan Sarkin Jama'a, a lokacin da yake hawan Sallah a Kafanchan din.

An ce, jami'an tsaro sun bude wuta, har ma an sami hasarar rayuka hudu da kuma jikkata.

Amma a cewar rundunar 'yan sandan jahar Kadunar, wata mata ce kawai ta mutu, bayan da mota ta buge ta.

Da ma ana zaman dar-dar a Kafanchan din, tun rikicin da ya biyo bayan zaben shugaban kasar.