Za'a kwashe 'yan kasashe waje daga Tripoli na Libya

Wasu jamaa dake ficewa daga Libya Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Wasu jamaa dake ficewa daga Libya

Hukumar kula da kaurar jama'a ta duniya ta ce tana shirin gudanar da wani aiki na kwashe dubban 'yan kasashen waje daga Tripoli, babban birnin Libya, yayinda fada ke kara kusantar birnin.

Kungiyar ta ce akwai ma'aikata 'yan kasashen waje da fadan ya rutsa da su, kuma suna son barin birnin yayin da 'yan tawayen ke durfafar shi.

A Yau 'yan tawayen su karbe iko da garin Garyan, Kudu da Tripolin, inda mutane suka yi ta shewa don murna.

'Yan tawayen sun ce sun kaddamar da sabon farmaki kan garin Ziltan, gabas da birnin Tripoli.