Faragaba akan makomar 'yan adawar Libya

Hakkin mallakar hoto Getty

'Yan Tawayan Libya sunce suna fargabar rayuwar mutane kamar dubu hamsin da dakaraun gaddafi suka tsare a watannin baya.

'Yan tawayen sunce watakila ana tsare ne da mutanen a wasu ramuka na karsashen kasa.

Sun kuma kara da cewa kawo yanzu mutane dubu goma sha daya ne kawai aka iya ganowa a cikin wadanda suka bace