Niger ta yi na'am da 'yan tawayen Libya

Gwamnatin Jumhuriyar Nijar ta ce ta yi na'am da gwamnatin 'yan tawayen Libya.

Niger dai wadda ke makwbataka da Libyar, na da daddadiyar dangantaka da gwamnatin kanar Gaddafi.

A wata sanarwa da ta bayar, wadda aka karanta a gidan rediyon kasar na Voix du Sahel, gwamnatin Nijar din ta ce za ta yi hulda da 'yan tawayen, amma ta yi kira ga bangarorin biyu da su ajiye makamai don a samu sukunin sassanta 'yan kasar.

A 'yan kwanakin da suka wuce dai, kasashen Afrika da dama ne, ciki har da Najeriya da Burkina Faso da kuma Chadi, suka amince da gwamnatin 'yan tawayen na Libya.