An kai hari a Jihar Kaduna

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Rahotanni daga jahar Kaduna a Nijeriya na cewa wasu wadanda ba a san ko su wanene ba, sun kaddamar da wani hari a gidan wani basarake a kudancin jihar.

Harin ya yi sanadiyar mutuwar mutane biyu da kuma jikkata wasu

An kaddamar da wannan hari ne a gidan hakimin Fadiya, na masarautar Bajju a garin Zonkwa, daya daga cikin garuruwan da aka tafka munanan rikici rikicen kabilanci bayan zaben shugaban kasa na watan Afrilu.

Da dama daga cikin mutanen garin na Zonkuwa dai a yanzu na gudun hijira a cikin garin kaduna tun bayan rikicin.