Obama ya yabi 'yan tawayen Libya

Shugaba Obama ya yaba wa al'ummar Libya, domin abinda ya kira gagarumar sadaukarwar da suka yi.

Ya ce, duk da cewa ana ci gaba da yaki, abinda 'yan Libyan ke nema na dab da fadawa hannunsu.

Shi ma Sakatare Janar na majalisar dinkin duniya Ban ki Moon, ya yi gargadin cewa, ya zama dole ga dukkan mambobin majalisar dinkin duniya da su yi biyayya ga kotun hukunta laifukan yaki ta duniya, wadda ta bada sammacin kama Kanar Gaddafi, da dansa saiful al islam da kuma babban jami'in tsaronsa na farin kaya.

Ya kuma kira wani taron gaggawa kan Libya wanda za a gudanar nan gaba a cikin wannan makon tsakanin Tarayyar Afrika, Kungiyar kasashen Larabawa, da kuma Tarayyar Turai.