Mutane 500 sun mutu a Sudan ta Kudu

Sudan ta kudu

Hukumomin Kasar Sudan ta Kudu sunce a kalla mutane dari biyar ne suka mutu a wani fada tsakanin wasu kabilu masu gaba da juna.

Lamarin dai ya faru jiya a jihar Jonglei, daya daga cikin yankunan kasar dake fama da matsalolin tsaro.

Yanzu kamar wata guda kenan da Sudan ta kudu ta samu 'yancin kanta kuma, matsalolin tsaro na daga cikin manyan kalubalen da ake fuskanta a kasar.