Scotland ta kare matakin data dauka akan Libya

Image caption Abdulbaset Al'megrahi da dan Moumar Gaddafi

Gwamnatin Scotland ta kare matakinda ta dauka shekaru biyu da suka gabata, na sakin mutumin kasar Libya da aka samu da laifin fasa jirgin Amurka a Lockerbie, wato Abdelbaset Al-Megrahi.

An saki Mr Megrahi ne daga gidan yari saboda an yi tsammanin cewa zai rasu cikin watanni biyu sakamakon cutar cancer da yake fama da ita, to saidai har yanzu yana nan da ran sa a Libya.

Wakilin BBC ya ce, masu suka, sun fusata a lokacinda suka ga Mr Megrahi a gangamin goyonbayan Kanar Gaddafi a watan jiya.

Ministan Scotland Alex Salmond, ya ce, sukar da aka rika yiwa gwamnati kasar a shekaru biyu sun wanke matakin data dauka.

Ya ce an dau matakin ne da kyakkyawar manufa.