Tawagar Majalisar dinkin duniya na gab da isa Syria

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Sakatare janarar na Majalisar dinkin duniya

Tawagar Majalisar dinkin duniya ta hukumar agaji na gab da isa Syria a yau, yayinda zanga zangar kin jinin gwamnatin shugaba Bashar al-Assad ke ci gaba.

Majalisar ta ce an baiwa tawagar damar shiga ko ina a kasar.

Rahotanni daga birni na ukku mafi girma a kasar ta Syriar wato Homs, na nuna cewa dakarun gwamnati sun bude wuta a yau asabar, duk da nanatawar da mahukunta kasar suka yi cewa, an dakatar da daukar matakan soji.

A bangare guda kuma matsin lamba na ci gaba da karuwa daga kasashen ketare kan shugaba Asad.