Manchester City ta yi galaba akan Bolton

Manchester City ta ci gaba da haskakawa a gasar Premier ta Ingila, bayan ta doke Bolton a wasan ta na biyu a kakar wasan bana.

Manchester City dai ta doke Bolton ne da ci uku da biyu.

David Silva ne dai ya zura kwallon farko, sannan sai Gareth Barry ya zura ta biyu, kafin Ivan Klasnic ya fanshewa Bolton kwallo guda.

Bayan an dawo hutun rabin lokaci ne dai Edin Dzeko ya zura ta uku sannan Kevin Davies ya kara fanshe guda.