Sabon shugaban Kotun daukaka kara a Najeriya

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Goodluck Jonathan

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya nada mai shari'a Dalhatu Adamu a matsayin mai rikon shugabancin kotun daukaka kara ta kasar.

Hakan ya biyo bayan shawarar da hukumar da ke sa ido kan al'amuran Shari'a ta Najeriya ta gabatarwa shugaban kasar ne, inda ta nemi da ya dakatar da shugaban kotun daukaka kara ta kasar Mai shari'a Ayo Salami daga aiki, tare da yi masa ritaya.

Wata sanarwa da ta fito daga kakakin gwamnatin kasar, Rueben Abbati, ta ce mai shari'a Dalhatu Adamu zai rike wannan mukamin ne kafin a nada sabon shugaban kotun daukaka kara ta kasar.

Wannan dai na zuwa ne yayin da kungiyar Lauyoyi ta Najeriyar ke fara taron ta na shekara- shekara, a yau Litinin a dai dai lokacin da Najeriyar ke fuskantar kalubale da dama da suka shafi martabar fannin shari'arta.