'Yan tawaye sun shiga fadar Gaddafi

Gaddafi Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Kanal Gaddafi ya shafe shekaru 42 yana mulki a Libya

Rahotanni daga Tripoli babban birnin kasar Libya, na cewa daruruwan 'yan tawaye sun shiga fadar Kanal Muammar Gaddafi, wacce ke Bab al-Azizya.

'Yan jaridar da ke binsu sun ce dakarun 'yan tawayen na harba bindigogi sama a cikin gidan domin murna.

Shiga gidan ya zo ne bayan shafe sa'o'i ana bata kashi. Babu tabbas kan ko Kanal Gaddafi da iyalansa suna cikin gidan.

Hotunan talabijin sun nuna 'yan tawayen na rusa mutum-mutumin Kanal Gaddafi da kuma hotunansa da tutocin gwamnatinsa a cikin gida. Suna kuma sace wasu kayayyakin.

Wakilin BBC Matthew Price a birnin Tripoli ya ce ana ganin hayaki na tashi a kusa da fadar Kanal Gaddafi. Amma har yanzu babu tabbas kan inda Gaddafin ya ke.

Bukatar kayan agaji

Kungiyar tsaro ta Nato ta ce mulkin kanal Gaddafi ya zama tarihi.

Kungiyar bayar da agaji ta Red Cross ta ce fadan da ake yi a birnin Tripoli ya haifar da matukar bukatar kayan agaji musamman magunguna da kuma ma'aikata.

Ta ce fararen hula da dama na daga cikin wadanda fadan ya ritsa da su, saboda yawancin fadan na faruwa ne a yankunan da fararen hula suka fi yawa.

Saif al-Islam ya bayyana

A kwai rahotannin da ke cewa jiragen yakin Nato na shawagi kasa-kasa a kan birnin na Tripoli.

A wani lamari mai ban mamaki, Saif al-Islam, dan Kanal Gaddafi, wanda ake kyautata zaton cewa shi ne zai gaje shi ya bayyana a birnin Turabulus a ranar Talata inda ya musanta ikirarin da 'yan tawayen Libya suka yi cewa sun kama shi.

Shi dai Saif al-Islam na cike ne da alfahari inda ya shaidawa BBC cewa dakarun gwamnati sun karya lagon 'yan tawayen bayan da suka yi musu kofar rago.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Saif aI-Islam yana ganawa da 'yan jarida

Ya jaddada cewa mahaifin sa, Kanal Gaddafi, na nan a Turabulus cikin koshin lafiya.

Ya ce kungiyar tsaro ta NATO ce kawai ke yada karairayi game da kamun na sa, amma a zahiri babu abin da ya same shi.

'Za mu koma Turabulus'

A yayin da ake ci gaba da dauki- ba- dadi na neman kwace iko a Turabulus, shugabannin 'yan tawaye sun ce sun yi shirin komawa birnin a gobe Laraba don kama aiki gadan- gadan na kafa sabuwar gwamnati.

Sai dai jagoran 'yan tawayen, Mustafa Abdel Jalil, ya ce matakin da ake ciki na da hadarin gaske saboda magoya bayan Kanal Gaddafi ka iya kai hare-haren ramuwar gayya.

Ya yi barazanar ajiye aiki matukar kwamandojin 'yan tawayen suka ki yin biyayya ga ka'idojin yakin da suke yi da gwamnatin Gaddafi.

Muhimman wurare a birnin Tripoli

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Karin bayani