Janye tuhumar da ake yi wa Strauss Kahn

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dominique Strauss-Kahn

Masu shigar da kara a kotun birnin New York da ke Amurka sun nemi alkali da ya janye tuhumar da ake yi wa tsohon shugaban Asusun Bayar da Lamuni na Duniya, Dominique Strauss Kahn.

An zargi Mista Strauss Kahn ne da cin zarafi, da kuma yunkurin yin fyade ga wata ma'aikaciyar otal din da ya zauna a New York.

Masu shigar da karar dai ba su da cikakkiyar shaidar karyata ikirarin da Mista Strauss Kahn ya yi cewa shi da matar sun amince kafin ya yi yunkurin yin lalata da ita.

A yau Talata ne ake zaton za a yi watsi da karar, sai dai Mista Strauss Kahn, wanda ake ganin shi ne zai kasance sabon shugaban Faransa, zai ci gaba da fuskantar tuhuma ta wani laifi da aka ce ya aikata a kasar.