Girgizar kasa ta shafi gabar tekun gabacin Amurka

An yi girgizar kasar a gabar gabashin Amirka, wadda ta shafi biranen Washington da New York, da kuma sauran garuruwa da birane a wani yanki mai fadi.

A Washington, ma'aikata sun bar ofisoshi sun bazama kan tituna.

An kwashe ma'aikata daga wasu sassa na ma'aikatar tsaron Amirka ta Pentagon, da fadar gwamnatin kasar ta White House, da majalisar dokokin kasar, da kuma dogayen gine-gine.

Jahar Virginia, wadda ke da tazarar wajejen kilomita dari da arba'in daga WAshington, ita ce cibiyar girgizar kasar, wadda bata kai maki shidda ba.

An ce an ji girgizar kasar a birnin Toronto na Canada.