An bukaci agajin abinci ga Somalia

A Najeriya, wata kungiyar kare hakkin farar-hula ta shiyyar Afirka ta yamma, wato West Africa Civil Society Organisation, ta yi wata ganawa da `yan jarida a Abuja game da halin kaka-nika-yi da al`umomin da ke yankin kusurwar gabashin Afirka suka samu kansu ciki a sakamakon bala`in yunwa da fari da ya abka musu.

Kungiyar ta ce miliyoyin jama`a ne ke cikin kunci kuma akwai bukatar gwamnatocin kasashen da ke nahiyar, da kuma masu sukuni su kai musu daukin gaggawa.

A cewar kungiyar, baya ga yankin kusurwar gabashin Afirka, akwai al`umomin da ke fama da masifar yunwa a wasu sassan nahiyar, cikinsu har da Najeriya.