Masu biyayya ga Gaddafi da 'yan tawaye na fafatawa

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Har yanzu dai ba'a san inda Kanal Gaddafi da iyalansa su ka shiga ba

Har yanzu masu biyayya ga Kanar Gaddafi na nuna wata yar bijirewa a Tripoli kwana daya bayan 'yan tawaye sun afka cikin harabar mazaunin Shugaban Libyar.

Wani wakilin BBC a cikin harabar ya ce ga alama mayaka 'yan gani kashe nin Gaddafi sun girke kansu a ciki, inda suke harbin yan tawayen, yayinda kuma masu biyayya gare shi a waje ke harba rokoki jefi jefi a cikin harabar.

Wannan dai na faruwa ne yayinda 'yan tawayen ke neman Kanar Gaddafin, suna masu cewar yana da muhimmanci su kama shi domin kawar da duk wata damar maida martani.

Ta fuskar diplomasiya kuma wakilan majalisar wucin gadi ta kasa ta yan tawayen Libyar na yin tattaunawa a yau a Qatar tare da jakadu daga kasashen yammacin duniya da kuma na yankin Gulf.

Daya daga cikin manyan yan majalisar wucin gadin, Mahmoud Jibril ya ce za su nemi Dola biliyan 2 da rabi na taimakon gaggawa.